A cewar Cibiyar Watsa Labarai ta Falasdinu, ta sanya ido kan ayyukan ‘yan gwagwarmaya 22 a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan, da suka hada da musayar wuta da sojojin mamayar Isra’ila da tashe-tashen bama-bamai da kalubalantar tsagerun yahaudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida, da kuma kai hare-haren daukan fansa kan sansanonin sojojin mamaya da suke sassa daban-daban na yankin.
A birnin Qudus, aka gwabza fada a garin Silwan da sansanin Qalandia, wanda ya hada da jifa da duwatsu da kuma fito na fito da mazauna garin.
A garin Ramallah, al’ummar garin Turmus Ayya sun mayar da martani kan harin da wasu tsagerun yahudawan sahayoniyya mazauna matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida suka kai musu.
Sannan an yi artabu da makami, ciki har da tayar da bama-bamai, a lokacin da sojojin mamaya suka kai farmaki kan garuruwan Arbouna, Faqoua, Araba da Ya’bad a birnin Jenin.
Kamar yadda ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka bude wuta kan wasu gungun tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a kusa da garin Salfit, kafin daga bisani su janye daga kan aniyarsu ta farma Falasdinawa.