Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Tilastawa Sojojin Yahudawan Sahayoniyya Daga Jabaliya

Bayan fuskantar mummunan martani daga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa, sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun janye daga sansanin Jabaliya Rahotonni sun bayyana cewa: Motocin yakin sojojin mamayar

Bayan fuskantar mummunan martani daga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa, sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun janye daga sansanin Jabaliya

Rahotonni sun bayyana cewa: Motocin yakin sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun janye daga sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya da sansanin soji da suka kafa a shiyar arewacin Zirin Gaza zuwa arewa maso gabashin yankin, bayan da suka fuskanci babbar hasarar rayuka da na kayayyakin yaki daga hare-haren  daukan fansa da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka mayar kansu.

Rahotanni sun kara da cewa: A halin yanzu haka jama’a sun koma sansanin Jabaliya bayan da sojojin yahudawan sahayoniyya suka janye daga yankunan, amma kwatsam sai ga jiragen saman yakin sojojin yahudawan sun kawo farmaki, inda suka din ga yin luguden wuta kan jama’a lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar mutane tare da jikkatan wasu na daban. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya yi nuni da cewa: Janyewar sojojin yahudawan sahayoniyya da motocin yakinsu daga arewacin Zirin Gaza zuwa kan iyakar gabashin yankin ya biyo bayan gwabza kazamin fada da suka yi ne da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa, lamarin da ya tilasta musu janyewa bayan da suka samu munanan hasarori na rayuka da kayan yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments