‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Jami’in Tsaron Iran A Garin Iranshahr

Wani jami’in tsaron Iran ya yi shahada sakamakon hari da makami da aka kai masa a garin Iranshahr da ke lardin Sistan and Baluchestan Rahotonni

Wani jami’in tsaron Iran ya yi shahada sakamakon hari da makami da aka kai masa a garin Iranshahr da ke lardin Sistan and Baluchestan

Rahotonni sun watsa rahoton cewa: Wani gungun mahara ‘yan ina ga kisa sun farma wani wani jami’in tsaro a safiyar yau da harbi da bindiga yayin da yake bakin aiki a garin Iranshahr lamarin da ya kai ga shahadarsa.

Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito cewa: Cibiyar Kafafen Yada Labarai ta ‘Yan Sanda ta gundumar Sistan da Baluchestan ta sanar da shahadan wani jami’in tsaro yayin da yake bakin aiki a safiyar yau, bayan wani hari da makami a Iranshahr.

A cewar sanarwar, jami’an tsaro na ci gaba da kokarin gano wadanda suka kai harin da kuma kama su. Cibiyar yada labarai ta ‘yan sanda za ta fitar da karin bayani game da lamarin daga baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted