Kakakin Majalisar dokokin kasar Yamen yayi tir da munafuncin da majalisar kungiyar tarayyar turai take kullawa da kuma sanya sunan kungiyar ansarullah cikin bakin suna, yace wannan matakin ya tona asirin munafunci da harshen damo da take nunawa
Yahya Ali Ahmed al raee ya jaddada cewa matakin da yan majalisar suka dauka kan kasar yamen bai wuce matakin siyasa ba na rufe laifukan yaki da kasar Sadiya ta tafka da sojojinta kan alummar kasar yamen
Kudurin baya bayan nan da majalisar kungiyar tarayyar turai ta fitar ya nuna harshen damo da munafunci, kuma yunkuri ne na murde gaskiyar matsayin gwamnatin yamen mai hedkwata a birnin sana’a da kuma yin watsi da alkawuran da ta sha bayarwa da kuma jajircewarta wajen tabbatar da tsaro a teku a matakin kasa da kasa
A ranar alhamis data gabata ne majalisar kungiyar tarayyar turai ta bayyana kungiyar gwagwarmaya ta ansrulla a matsayin kungiyar ta’adda, da ya hada da dukkan bangarenta na siyasa da na soji, da shugabancinta da sauran abubuwan da suka shafi tsaro na soji