Yamen Tace Farmakin Aqsa Ta Zama Ta Bayyana Raunin Isra’ila

shugaban kungiyar Ansarullah ya ce ambaliyar aqsa ta nuna rauni isra'ila ta kuma sanya tsarin gwagwarmar falasdinu

shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yamen Abdulmalik al-huthi ya jinjinawa harin farmakin Aqsa da aka kai kuma ya bayyanata a matsayin daya daga cikin abubuwan tarihin falasdinu da ba zaa taba mantawa da shi ba, yace harin ba zata da aka kai ya girgiza gwamnatin isra’ila  kuma ya tona asirin raunin da  take da shi

A lokacin da yake jawabi ta gidan talabijin din kasar yamen a yammacin jiya laraba kan tunawa da cika shekaru 3 da kai harin ambaliyar Aqsa  a Isra’ila, abdulmalik huthi ya bayyana harin  a matsayin muhimmiyar sauyi a gwagwarmayar da falasdinawa suka shafe shakaru da dama suna yi na kalubalantar mamayar isra’ila

Haka zalika ya kara da cewa harin ambaliyar Aqsa ya samar da wata dama ga kasashen musulmi da su sauke nauyin da ya rataya a wuyanzu na jinkai da nuna dan adamtaka ga alummar falasdinu,

A daidai lokacin da kasar Amurka birtaniya da sauran kasashen yammacin duniya ke kokarin taimakawa gwamntin isra’ila kan harin ambliyar Aqsa , amma kasashen musulmi sun kasa taimakawa alummar falasdinu da ake zalunta

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted