Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan Ilimi ya bayyana cewa: Yara miliyan 14 ne ba sa zuwa makaranta a Sudan
Sudan na fuskantar ɗaya daga cikin mawuyacin halin a fagen ilimi ya fi kamari a duniya, inda miliyoyin yara da iyalai da aka kora daga gidajensu ke rayuwa cikin mawuyacin hali wanda ya hana wa tsararraki da dama ‘yancinsu na ilimi. Wannan rikicin yana faruwa ne a tsakanin yaƙin da ya gurgunta cibiyoyin ilimi tare da ƙara ta’azzara matsalar jin kai a faɗin ƙasar.
Nismi Manigat, Babban Jami’in Haɗin Gwiwa na Ilimi na Duniya, ya bayyana cewa: Sudan na fuskantar “ɗaya daga cikin mawuyacin hali a duniya,” yana mai lura da cewa kimanin yara miliyan 14 ba sa zuwa makaranta, wanda ke wakiltar mafi girman rikicin da aka taɓa fuskanta a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al Jazeera, ya bayyana cewa: Waɗannan alkaluman suna una “ɓacin rai da damuwa” kuma suna nuna gaskiyar abin da ya faru na iyalai da aka kora da ke fafutukar rayuwa, yayin da ‘ya’yansu ke fuskantar rashin damar samun ilimi da ingatacciyar rayuwa ta yau da kullun.
Manigat ya ƙara da cewa: Dole ne al’ummar duniya ta yi duk abin da za ta iya, don magance wannan mummunan yanayi, wanda ke barazana ga makomar al’umma baki ɗaya.