Yakin Iran Ya Jawo Asarar Dala Biliyan 47 Ga Amurka

Wannan kiyasin bai hada da sansanonin sojojin Amurka da aka lalata a Yammacin Asiya sanadin hare haren Iran.

Wani sabon kiyasi da rundinar sojin Amurka ta CENTCOM, ta fitar ya nuna cewa kasar ta yi asarar Dala Biliyan 47.1 a yankinta da Iran.

Adadin ya karu idan aka kwatanta da kimanin dala biliyan 37.5 da Sakataren Yaki na Amurka Pete Hegseth ya sanar wa ‘yan majalisa watanni uku da suka gabata.

Wannan kiyasin bai hada da sansanonin sojojin Amurka da aka lalata a Yammacin Asiya sanadin hare haren Iran.

Ofishin Kasafin Kudi na Majalisar Dokokin Amurka ya yi gargadi a watan da ya gabata cewa yakin zai iya kashe Washington tsakanin dala biliyan 2 zuwa dala biliyan 3 a kowane wata muddin ya ci gaba.

Gwamnatin Amurka ta kuma nemi karin biliyoyin daloli daga Majalisa, yayin da ‘yan Jam’iiyar Democrat ke matsa wa Hegseth lamba ya yi cikakken bayani game da kudaden da wannan rikici ya jawo.

Yakin Amurka da Isra’ila da Iran ya fara ne a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 3,000 da kuma raunata sama da 32,000.

A lokacin wannan farmakin, Iran ta kare kanta ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin Amurka da cibiyoyinta a Yammacin Asiya.

Sanatocin Amurka sun yi imanin cewa kiyasin asarar da yakin ya yi ga kayayyakin more rayuwa na soja abu ne da dole Amurkawa ya kamata su samu cikakken bayyani akansa.

An tura sojojin Amurka sama da 50,000 a yakin da ake yi da Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted