‘Yan Sahayoniyya Suna Ci Gaba Da Tserewa Daga Isra’ila

Yahudawan Sahayoniyya suna ci gaba da tsarewa daga Isra’ila kuma tsarewar da babu dawowa ba Yayin da Fira Ministan Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu

Yahudawan Sahayoniyya suna ci gaba da tsarewa daga Isra’ila kuma tsarewar da babu dawowa ba

Yayin da Fira Ministan Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ke alfahari da nasarorin da ya samu da kuma canza yanayin Gabas ta Tsakiya, adadin Yahudawan Sahayoniyya da suke tsarewa daga yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya bayyana wani yanayi na daban, wanda ke nuna girman rikicin cikin gida a Isra’ila, yayin da gwamnatin Isra’ila take kara ta’azzara yaƙe-yaƙenta a fannoni daban-daban.

A cewar jaridar Ma’ariv ta Haramtacciyar kasar Isra’ila, a wani rahoto da Cibiyar Bincike da Bayanai ta Knesset ta fitar ya nuna cewa: Adadin wadanda suka dawo Isra’ila ya ragu da kashi 53% a cikin ‘yan shekarun nan.

Rahoton ya nuna cewa: Dubban daruruwan Yahudawan Sahayoniyya sun fice daga Isra’ila kuma ba zasu dawo ba, yana mai lura da cewa wannan raguwar ta fara ne a shekara ta 2023 kuma ta ci gaba tsakanin shekara ta 2021 da 2024.

A cewar jaridar, adadin wadanda suka dawo ya ragu daga kimanin 8,000 a shekara ta 2020 zuwa kimanin 3,800 kacal a shekara ta 2024, raguwar kashi 53%, mafi karancin adadin wadanda suka dawo a cikin ‘yan shekarun nan, tare da raguwar da yanayin ke kara tsananta a shekara ta 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted