rahotannni sun bayyana cewa yahudawa yan share wuri zauna da sojojin mamaya na isra’ila sun kashe wani matashi bafalasdine dan shekaru 19 da haihuwa a gabar yammacin kogin jodan da aka mamaye, mutane biyu ke nan da aka kashe a cikin sa’oi 48 adaidai lokacin da ta’addancin yahudawa yan share wuri zauna yake kara yawaita a cikin wannan shekarar
Matashin da aka kashe dan shekaru 19 mai suna Baha sami al-natsheh an harbe shi ne a kauyen kobar dake arewacin Ramallah, kamar yadda hukumomin yanki da kungiyar bada agaji ta red cresent suka bayyana da gangan yahudawa yan share wuri zauna suka hana jami’in lafiya isa inda yake domin su bashi kulawa daga raunin da ya samu, inda suka bari yayi ta zuban jinni har ya mutu a wajen.
kuma lamarin ya faru ne alokacin da matashin a garin kubar yayi kokarin bude shinge da yahudawa yan share wuri zauna suka sanya, inda sanya irin wannan shingaye ya zama ruwan dare ga yahudawan a matsayin wata dabara na mamaye kauyukan falasdinawa da kuma hana su yanci zirga-zirga da takurawa mazauna yankunan a garuruwansu.