Search
Close this search box.

Yahudawa Masu Tsatsauran Ra’ayi Na Kona Gonakin Falastinawa

Yahudawa ‘yan kama waje zauna na Isra’ila sun kona filayen noma na Falasdinawa da ke kusa da birnin Nablus a Yammacin Gabar Kogin Jordan da

Yahudawa ‘yan kama waje zauna na Isra’ila sun kona filayen noma na Falasdinawa da ke kusa da birnin Nablus a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, inda suka mayar da amfanin gonakin hatsi da itatuwan zaitun zuwa toka.

Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, da gangan wasu gungun Yahudawa ‘yan kama waje zauna na Isra’ila sun ƙona gonaki a garin Bayt Furik da ke gabashin birnin Nablus.

Wutar ta ƙone wani yanki mai yawa na shukar hatsi da itatuwan zaitun, duk da kokarin da Falasdinawa suka yi na kashe ta, in ji shaidun.

A gefe guda kuma, matsugunan Yahudawa ‘yan kama waje zauna na Isra’ila a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan sun lalata amfanin gonakin Falasdinawa ta hanyar kiwon tumakinsu a cikin gonakin, kamar yadda majiyar kasar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Wani lamari da ya faru a kudancin Gabar Yammacin Kogin Jordan ya faru lokacin da wasu matsugunan Yahudawa ‘yan kama waje zauna na Isra’ila suka lalata amfanin gona a kasar Falasdinu yayin da suke kiwon tumakinsu, in ji majiyoyin cikin gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments