Hamas : Babu Wani Ci Gaba A Tattaunawar Tsagaita Wuta A Gaza Da Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bakin wani jami’inta ta bayyana cewa babu wani ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila. Osama Hamdan ya ce har yanzu a shirye Hamas take a cimma matsaya mai kyau” kan shawarar tsagaita bude wuta ta kawo karshen yakin kamar yadda ya bayyana a wani taron […]
Isra’ila Ta Kashe Karin Falasdinawa 40 A Cikin Sa’o’I 24 Da Suka Gabata

Ma’aikatar lafiya a Gaza a sanar da cewa adadin Falasdinawan da sukayi shahada sanadin hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba ya haura zuwa Dubu 37 da Dari 834. Ko a cikin sa’o’I 24 da suka gabata falasdinawa 40 suka rasa rayukansu sanadin hare-haren na Isra’ila a Gaza. Ko baya ga wadanan alkalumman da […]
Zaben Iran : ‘Yan Takara A Zagaye Na Biyu Zasu Fara Yakin Neman Zabe Daga Ranar Lahadi

A Iran, yan takara da zasu fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar zasu fara yakin neman zabe daga gobe Lahadi. Yakin neman zaben zai kawo karshe sa’o’I 24 gabanin kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar. A ranar Juma’a mai zuwa 5 ga watan Yuli ne za’a gudanar […]
‘Yan Takara Bakwai Na Fafatawa A Zaben Shugaban Kasa A Mauritania

A Mauritami ‘yan takara bakwai ne suka fafata a zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa yau Asabar. Daga cikin ‘yan takaran har da Shugaba Mohamed Ould Ghazouani mai barin gado. Sauran jiga-jigan ‘yan takaran sun hada da mai rajin kare hakkin bil adama Biram Dah Abeid, wanda ya zo matsayi na biyu a zabukan […]
Bagheri Kani: Dangantaka Tsakanin da Saudiyya Na Ci Gaba Da Kara Bunkasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya bayyana yadda alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiya take ci gaba da kara bunkasa a dukkanin bangarori, yana mai jaddada cewa Tehran da Riyadh sun kudiri aniyar ci gaba da yin aiki tare a fagage da dama domin ci […]
Isra’ila Na Ci Gaba Da Yin Ta’annuti A Yankin Rafah Da Ke Gaza

Sojojin Isra’ila sun sake kutsawa cikin yankuna biyu na arewaci da kudancin Gaza, kuma jami’an kiwon lafiyar Falasdinu sun ce harin tankokin yaki a Rafah ya kashe akalla mutum 11. Mazauna yankin da kafafen yada labarai na cikin gida sun ce tankokin yaki sun kara yin yamma zuwa unguwar Shakoush da ke Rafah, lamarin da […]
Yahudawa Masu Tsatsauran Ra’ayi Na Kona Gonakin Falastinawa
Yahudawa ‘yan kama waje zauna na Isra’ila sun kona filayen noma na Falasdinawa da ke kusa da birnin Nablus a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, inda suka mayar da amfanin gonakin hatsi da itatuwan zaitun zuwa toka. Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, da gangan wasu […]
Iran: Za A Je Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa Tsakanin Jalili Da Pezeshkian

A kasar Iran za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu bayan da dukkanin ‘yan takarar suka kasa samun cikakkiyar nasara ta lashe zaben a zagayen farko, in ji kakakin hedkwatar zaben. Mohsen Eslami ne ya sanar da sakamakon a ranar yau Asabar a wani taron manema labarai wanda gidan talabijin na kasar […]
Iran: Zaben Shugaban kasa na ci gaba da jan hankalin kafofin yada labarai na duniya

Kafofin yada labarai na yanki da na kasa da kasa sun ba da labarin da ya shafi wannan al’amari daga sa’o’i na farko na gudanar da zaben shugaban kasa a Iran. a cewar babban daraktan yada labaran harkokin wajen ma’aikatar al’adu da shiryarwar muslunci, ‘yan jarida sama da 500 daga gidajen yari da kuma na […]
An Kammala Zaben Shugaban Kasa A Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Lami Lafiya

Zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Iran a jiya Juma’a ya samu fitowar jama’a sosai, lamarin da ya sa aka kara tsawaita lokacin zaben Zaben shugaban kasa a Iran shi ne karo na 14 da aka gudanar a kasar tun bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci, inda zaben ya samu halartar jama’a […]
Makaddashin Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Takwaransa Na Saudiyya

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da takwaransa na Saudiyya kan batutuwan da suka shafi kasashensu da kuma batun Falasdinu Mukaddashin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ali Baqiri ya tattauna da ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ta hanyar wayar tarho, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashensu […]
Gwamnatin Amurka Ta Gargadi Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kai Hari Kasar Lebanon

Gwamnatin Amurka ta gargadi haramtacciyar kasar Isra’ila kan kaddamar da hare-hare kan kasar Lebanon Jami’an gwamnatin Amurka sun gargadi ministan tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, Yo’av Gallant, game da duk wani yunkurin mamaye wani yanki na kudancin Lebanon, saboda hakan zai haifar da barkewar yakin basasa a yankin. Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Ha’aretz” ta […]
Sojojin Yemen Da Hadin Gwiwar ‘Yan Gwagwarmayar Iraki Sun Kai Hari Kan Jirgin Ruwan Waler

Sojojin Yemen sun kai hari kan jirgin ruwa “Waler” a wani farmakin hadin gwiwa da dakarun kasar Iraki A wata sanarwa da sojojin kasar Yemen suka fitar, a jiya Juma’a, sun bayyana kaddamar da wani harin hadin gwiwa tare da ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki, inda suka yi barin wuta kan jirgin ruwan “Waler” ta hanyar […]
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Kasar Nijar

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta jajanta wa Nijar kan wadanda harin ta’addancin ya rutsa da su a kasar Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da harin ta’addanci da aka kai a ranar Talata a yankin Tillaberi na jamhuriyar Nijar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkata wasu […]