Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya.
Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot.
A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka.
Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya Alhamis dai rundunar sojan kasar ta Lebanon ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa; Duk da cewa a akwai tsagaita wutar yaki amma Isra’ila tana ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon ta kasa, ruwa da kuma sama.” Sanarwar ta kuma ce; Abinda Isra’ilan take yi,barazana ce ga zaman lafiya a cikin Lebanon da kuma wannan yankin.
Haka nan kuma rundunar sojan kasar ta Lebanon ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya suna ci gaba da kai wa mutane hare-hare a garuruwan kudancin Lebanon da kuma yankin Bik’a.
A cikin wannan halin, mutanen kudancin kasar ta Lebanon suna ci gaba da komawa garuruwansu duk da cewa suna fuskantar hastarin kai musu hari daga sojojin mamaya.
Tun a ranar 26 ga watan Nuwamba ne dai aka tsagaita wutar yaki a tsakanin Lebanon da HKI bisa cewa za ta janye daga wuraren da ta yi kutse a cikin kwanaki 60, sai dai kuma hakan ba ta faru ba. Kungiyar Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnati da ta yi amfani da hanyoyin diplomasiyya domin tilastawa ‘yan mamayar janyewa, kafin a shiga wata magana ta daban.