Wulayati: Amurkawa Suna Biyan Kudin Cacar Da Trump Ya Shiga

Mai ba da Shawara ga Jagoran Juyin Juya Hali ya bayyana cewa: A yau, iyalai ‘yan Amurka suna biyan kuɗin cacar da shugabanninsu ya shiga

Mai ba da Shawara ga Jagoran Juyin Juya Hali ya bayyana cewa: A yau, iyalai ‘yan Amurka suna biyan kuɗin cacar da shugabanninsu ya shiga da tsabar kuɗi

Ali Akbar Wulayati, mai ba da shawara ga Jagoran Juya Juya Halin Musulunci kan harkokin ƙasashen duniya, ya yi ikirarin cewa: Daidaiton yanki ya canza, kuma a yau al’ummar Amurka suna biyan kuɗin cacar da shugabanninsu ya wurga kansa ciki.

Wulayati ya rubutu a shafinsa na sada zumunta game da sakamakon takunkumi da killacewar Amurka da ta sanya wa Iran ga al’ummar Amurka cewa: “Scott Besnett yana magana game da takunkumin tattalin arziki da aka sanya wa Iran, Trump yana alfahari da toshe hanyoyin jiragen Ruwan Iran, kuma Sanata Cornyn yana magana game da tsadar rayuwa ga al’ummar Amurka.”

Ya ci gaba da cewa, “A jajiberin cikan shekaru 1953, kuma bayan shekaru 73, gaskiya ta bayyana: daidaiton yanki ya canza, kuma a yau al’ummar Amurka suna biyan kuɗin cacar shugabanninsu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted