WHO, ta nuna kaduwa da abin da ke faruwa a Gaza

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza.

Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai.

Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da rashin tabaka komai na taimaka wa jama’a a zirin Gaza.

“Muna wargaza tunani da jikin yaran Gaza, ga yunwa ga yaran Gaza, idan ba mu dauki mataki ba, za mu shiga cikin abin da ke faruwa a idanunmu,” in ji shi.

A gobe Juma’a ne za a cika watanni biyu na hana shigar da kayan agaji da sojojin Isra’ila suka yi a zirin Gaza baki daya.

Tun a ranar 2 ga Maris, ba a ba da izinin shigar da kayan agajin jin kai ba, a matakin da Isra’ila ta ce na tilasta wa kungiyar Hamas ne sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin ba zata na ranar 7 ga watan Oktoba 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments