Iran da Nijar sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa

Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki. An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na Iran 2025, karo na bakwai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka fara a birnin Tehran a ranar Litinin. Mohammad Atabak, ministan masana’antu, ma’adinai, da kasuwanci na Iran; da Mohammad […]
WHO, ta nuna kaduwa da abin da ke faruwa a Gaza

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai. Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da […]
An sauya ranar tattaunawa ta hudu tsakanin Iran da Amurka

Iran ta sanar da cewa an sauya ranar tattaunawa karo ta hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington da Tehran a ranar Asabar mai zuwa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar […]
Amurka ta sake kai Hari a yankunan Saada da Hudaidah na Yemen

Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis. Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun […]
Iran ta yi Allah-wadai da sabon takunkumin da Amurka ta lafta mata

Iran ta yi tir da Allah-wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta lafta mata. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce matakin wata babbar alama ce da ke nuna cewa Washington ba ta da kyakyawar niyya, hasali ba abar yarda ce ba. Sanarwar ta bayyana karara cewa Iran ba […]
Amurka Ta Kakabawa Kamfanonin Da Suke Hulda Da Iran Bangaren Man Fetur

A dai-dai lokacin da kasashen Amurka da JMI suke ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliya ta Iran gwamnatin Amurka a jiya Laraba ta dorawa kamfanoni da mutanen da suke mu’amala da JMI a bangaren man Fetur takunkuman tattalin arziki. Da dama daga cikin wadannan kamfanoni na kasar China ne. Jaridar ‘the Nation’ ta […]
Iran Tace Samar Da Kasar Falasdinu Mai Cikekken Yenci Ba Abin Tattaunawa Bane

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa samar da kasar Falasdinu mai cikekken yenci , kuma da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar, hakkin Falasdinawa ne wannan babu tattaunawa a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jakadan kasar Iran na din din din a MDD Amir Said Iravani yana fadar […]
Amurka Da Ukraine Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyar Da Aka Dade Ana Saurarunta Dangane Da Ma’adinai

Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa […]
Dakarun IRGC Na JMI Sun Kaddamar Da Sabon Kwale-Kwale Mai Cilla Makamai Masu Linzami

Rear Admiral Alireza Tangsiri babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC ya bayyana haka ne a jiya a bikin ranar “Tekun farisa’ ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kwale-kwalen mai sauran kilomita Knots 116 na ruwa wanda yayi dai-dai da kilomita 215 / a ko wace sa’a yana da […]
Syria: Adadin Wadanda Aka Kashe A Rikicin Bangaranci Sun Kai 70

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta nuna kin amincewarta da tsoma bakin kasashen waje a rikicin da kasar take fuskanta. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta kuma ce; gwamnatin kasar za ta kare dukkanin ‘yan kasar. Kasar Syria tana fuskantar fada a tsakanin ‘yan Duruz da kuma sojojin gwamnatin kasar a yankin Sahanaya […]
Dubban Mutanen Burkina Faso Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Shugaban Kasa Ibrahim Traore

Kwanaki kadan bayan wani furuci daga babban jami’in sojan Amurka a Afirka akan shugaban kasar ta Burkina, dubban mutanen kasar sun yi gangami na nuna goyon bayan Kaftin Ibrahim Traore Gangamin na mutanen kasar Burkina Faso, ya biyo bayan maganganun da su ka fito daga kwamandan sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley wanda ya […]
Arif: A Shirye Muke Mu Sabunta Sana’o’in Sudan

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta yi aiki da Sudan domin bunkasa sana’o’inta. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya furta haka ne dai a lokacin da […]
Iran: Makamin Nukiliya Ba Ya Cikin Akidar Tsaron Kasar Iran

Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran. Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman […]