Shirin Majalisar Dinkin Duniya Na Samar Da Abinci ( WFP) ya fitar da gargadi akan cewa, yankin gabashin DRC yana fama da matsananciyar yunwa.
Daraktar cibiyar ta WFP a kasar ta DRC Cynthia Jones ce ta yi wannan gargadin yana mai kara da cewa; Da akwai iyalan da suke tsallaken cin abinci, bayan da su ka sayar da kayan gidansu da kuma dabbobin da su ka mallaka.”
Hukumar da yake kula da wadatar abinci ( IPC) ta ce da akwai mutanen da adadinsu ya kai miliyan 25 da suke cikin matakin karshe na yunwa, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3 da suke cikin hatsari.
Hukumar ta MDD ta kuma ce, a halin yanzu mutane suna ta mutuwa saboda babu abinda za su ci a gabashin DRC.
Karancin Abincin da yankin na gabashin DRC yake fama da shi, yana da alaka da fadan da ake yi a tsakanin ‘yan tawayen M23 da sojojin gwamnati a yankin. Gwamnatin DRC dai tana tuhumar Rwanda da cewa ita ce mai goyon bayan kungiyar ‘yan tawayen ta M23 da makamai da kuma sojoji.
Gwamnatin Kigali dai ta sha karyata wannan zargin da ake yi mata.
A sanadiyyar rikicin yankin, mutane miliyan 5. 2 su ka bar gidajensu,a cikinsu da akwai mutane miliyan 1.6 a cikin wannan shekarar kadai.
Cibiyar ta ( WFP ) ta yi kiran gaggawa ga duniya da a kai dauki ga mutanen wannan yankin na gabashin DRC.