Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, […]
Kasashen (AES) za su hanzarta kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro

Ministocin tsaro na kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun yunkuri anniyar kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa, wacce zata tunkari magance barazanar ta’addanci mai nasaba da kungiyoyin JNIM da ISIS a yankin Sahel. Kasashen sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a Niamey karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani da […]
Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump

A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa zargin gwamnatin kasar da kauda kai kan kisan da ake wa kiristoci a kasar. Masu zanga-zanga a Kano, dake arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai da barazanar da kuma yin […]
Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin El-Fasher

Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da mummunan ta’addancin da aka aikata kan fararen hula a yankin El-Fasher na Sudan. Ofishin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ya yi gargadin cewa El-Fasher ya zama birnin makoki a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare masu muni, wanda hakan […]
Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila

A Labanon akalla mutane uku ne suka mutu sannan goma sha daya suka jikkata a hare-haren jiragen sama marasa matuka na Isra’ila a kudancin Lebanon, wanda ya sake nuna yadda Isra’ilar ke keta yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin suka cimma. A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa na Lebanon (NNA), an kashe ‘yan’uwa biyu […]
An Kafa Mutum-mutumin Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran

A wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a nan birnin Tehran an kafe Mutum-mutumin tarihi na sarkin daular Roma Velarian wanda aka kamo shi a matsayin fursunan yaki a zamanin Daular Sasaniyawa, ya kuma durkusa a gaban sarki Shahpur 1. Kafe Mutum-mutumin da aka yi, yana a karkashin jaddada matsayar Iran na cewa, al’ummarta ba […]
Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati

Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su […]
Wasu Kasashe Takwas Sun Bukaci Ganin An kama Benjamine Netanyahu

Wasu Karin kasashe takwas sun yi kira da a kama Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamine Netanyahu saboda laifukan yakin da ya aikata. Kasashen Turkiya, Norway, Italiya, Canada, Slovenia da Lithuania, sun bayyana cewa a shriye suke su kama fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila. A kasar Turkiya mai shiga da kara na birnin Istanbul […]
WFP: Ana Fama Da Matsananciyar Yunwa A Gabashin DRC

Shirin Majalisar Dinkin Duniya Na Samar Da Abinci ( WFP) ya fitar da gargadi akan cewa, yankin gabashin DRC yana fama da matsananciyar yunwa. Daraktar cibiyar ta WFP a kasar ta DRC Cynthia Jones ce ta yi wannan gargadin yana mai kara da cewa; Da akwai iyalan da suke tsallaken cin abinci, bayan da su […]
Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu. Da yake magana bayan dawowarsa daga […]
Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa

‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata. Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi […]
Martanin Iran ya haddasa wa Isra’ila hasarar fiye da Dala Miliyan 200

Hare-haren daukan fansa da Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar janyo hasarar dala miliyan 200 Harin da aka kai wa matatun mai na Haifa na ɗaya daga cikin ayyukan da Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya ga harin da Isra’ila ta kai a lokacin yaƙin kwanaki 12. Shirin “Lambar” a […]
Biden Ya Caccaki Trump Bisa Tuhumarsa Da Kawo Barna

Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya […]
Masar da Rasha sun tattauna batutuwan tsagaita wuta a Gaza da kuma Sudan

Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar […]