Wata Sabuwar Arangama Ta Kunno Kai Tsakanin Sojojin Sudan Da Dakarun Kai Daukin Gaggawa

An gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa a birnin Khartoum da Darfur Rahotonni sun bayyana cewa: Sudan ta sha fama

An gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa a birnin Khartoum da Darfur

Rahotonni sun bayyana cewa: Sudan ta sha fama da kazamin artabu tsakanin sojoji da Dakarun kai daukin gaggawa musamman a biranen Khartoum babban birnin kasar da kuma yankin Darfur, a daidai lokacin da bangarorin biyu ke amfani da jiragen sama marasa matuka ciki kan junansu.

Tun daga wayewar garin yau Laraba, birnin Bahri da ke arewacin birnin Khartoum, ya fara fuskantar kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, kuma sojojin sun kai wani kazamin farmaki a ci gaba da kai hare-hare kan Dakarun kai daukin gaggawa a unguwar Shambat da ke tsakiyar birnin Bahri.

Wata majiyar soji ta shaidawa gidan talabijin na Aljazeera cewa: Sojojin Sudan sun samu nasarar kutsawa cikin yankunan birnin Bahri, kamar unguwannin Shambat da Al-Ezbah, kuma majiyar ta nuna cewa: Dakarun kai daukin gaggawa sun koma yankunan Hillat Hamad da Al-Sha’abiyya.

Sojojin Sudan na neman damar kutsawa cikin birnin Bahri da ke makwabtaka da rundunar sojojin kasar a birnin Khartoum, wanda dakarun kai daukin gaggawa suka killace tun bayan barkewar yakin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments