Wata kotu a Birtaniya ta yanke wa wata mata hukuncin dauri a gidan yari da ta yi kira da a tarwatsa wani Masallaci a kasar
Kotu ta kasar Birtaniya ta yanke wa matar ‘yar kasar hukuncin daurin watanni 15 a gidan yari bisa samunta da laifin yin kira da a tada bam a wani masallaci tare da kashe wadanda ke ciki a wani sako da ta wallafa a shafukan sada zumunta.
A cewar jaridar The Telegraph ta Birtaniya, hukuncin ya zo ne bayan Julie Sweeney yar shekaru 53 daga birnin Cheshire na kasar Birtaniya ta amince da laifin wallafa wani sako na tunzura jama’a a shafin rukunin Facebook da ya kunshi mutane sama da 5,000.
Jaridar ta bayyana cewa, kiran da Sweeney ta yi na kai harin bam kan masallacin, ya zo ne a matsayin tsokacinta kan wani hoto da aka buga a cikin rukunin masu aikin sa kai na turawa da ‘yan Asiya da suke aikin tsaftace wani masallaci sakamakon cin zarafin musulmi da bakin haure da Biritaniya ta shaida bayan kashe ‘yan mata 3 a ranar 29 ga watan Yuni.