Wasu ‘yan kasar Ghana biyu sun kai kara a kotun Duniya

 A ranar 15 ga watan Yuli ne mutanen biyu ‘yan kasar Ghana da su ne tsohon kakakin gwamnati akan tsaro, Gelgrif Dankwaa da kuma jami’i

 A ranar 15 ga watan Yuli ne mutanen biyu ‘yan kasar Ghana da su ne tsohon kakakin gwamnati akan tsaro, Gelgrif Dankwaa da kuma jami’i mai Nazari akan harkokin tsaro da ta’addanci Emmanuel Kotin su ka shigar da kara a gaban kotun.Bayanin shigar da karar ya kunshi cewa,        ” Hare-haren na Afirka Ta Kudu akan ‘han hijira an yi su ne a tsare kuma da yawa,” tare da zargin gwamnatin shugaba Cyril Ramaphosa da kin hana masu aikata laifukan da yin kisa da sata akan ‘yan hijira, kuma ba a hukunta wadanda su ka aikata laifukan ba.

A cikin watannin bayan nan, kasar Afirka ta kudu ta rika fuskantar kai wa ‘yan hijira hare-hare har da kashe wasu daga cikinsu ‘yan Afirka da sace dukiyarsu a gidajensu. Hare-hare sun tilastawa gwamnatocin kasashen Afirka kwashe ‘yan kasashensu da ake nunawa tsangwama. A gefe daya, gwamnatin kasar ta Afirka Ta Kudu,ta bakin ma’aikatar alakar kasashen waje, ta yi watsi da wannan zargin da ake yimata, tare da bayyana cewa tana da cikakken tsari na fada da nuna wariya da dukkanin nau’o’inta.Sai dai ya zuwa yanzu kotun manyan laifukan ba ta zartar da cewa za ta bude bincike akan karar da aka shigar a gabanta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted