Wasu Shugabannin Turai Sun Yi Barazanar Ladabtar Da Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar

Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta

Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar matakin hukunta Isra’ila.

Wannan bayani dai ya samu karbuwa daga fadar shugabancin hukumar cin kwarya-kwaryan gashin kan Falasdinawa da kungiyar Hamas, amma fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shi. Wannan dai ya zo daidai da gargadin da kasashen duniya suka yi na fuskantar bala’in jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza sakamakon killace yankin da bullar masifar yunwa da ake ci gaba da yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted