Washington Post: Rikici tsakanin Biden da wasu ‘yan jam’iyyar Democrat ya kara tsananta

Jaridar Washington Post ta ruwaito wani rahoto, game da rikicin siyasa da ke kara ruruwa ga shugaban Amurka Joe Biden, tare da karuwar ‘yan jam’iyyar

Jaridar Washington Post ta ruwaito wani rahoto, game da rikicin siyasa da ke kara ruruwa ga shugaban Amurka Joe Biden, tare da karuwar ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilai da suke yin kira ga shugaban da ya janye daga takara a zabe mai zuwa.

Jaridar ta yi nuni da cewa wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar Democrat 4 a majalisar wakilai yayin wata ganawa ta sirri da shugabannin jam’iyyar Democrat a majalisar wakilai suka gudanar, sun bayyana cewa ya kamata Biden ya sauka, bisa ga imaninsu.

A cewar mutane biyu da suka halarci zaman, wakilan su ne Jerry Nadler (New York), Adam Smith (Washington), Mark Takano (California), da Joseph Morell (Democrat daga New York), yayin da suka hade da sauran ‘yan Democrat da cikin Majalisar wakilai wadanda suka fito fili suka yi kira ga Biden da ya yi watsi da yunkurinsa na sake tsayawa takara, domin kuwa sun yi imanin cewa Donald Trump zai kayar da shi.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, Biden da mukarrabansa sun kara dagewa cewa ba zai janye ba yayin da yakin neman zabe ke ci gaba a fadin kasar.

A ‘yan kwanakin da suka gabata, shugaban na Amurka ya sanar da cewa “zai ci gaba da kasancewa a wannan takarar ta neman shugabancin kasar har zuwa karshe.” Ya ce: “Na ce da babbar murya: Ba wanda zai kore ni daga takara,” kamar yadda  kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya ruwaito

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments