Jirgin Ruwan Dakon Mai Na Uku Ya Kama Da Wuta A Hormuz

Wani jirgin dakon man fetur na uku ya kama da wuta mai tsanani a mashigar tekun Hormuz Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), ta

Wani jirgin dakon man fetur na uku ya kama da wuta mai tsanani a mashigar tekun Hormuz

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), ta fitar da wata sanarwa cewa: Wani jirgin ruwan man fetur na uku ya bi ta kan wata nakiyar ruwa a yau wanda ya janyo tashin gobara kan jirgin.

Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya ruwaito cewa: Sashen Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ya sanar da cewa: Wani jirgin ruwa na uku ya afka kan wata nakiyar ruwa a yau da ya janyo tarwatsawar nakiyar tare da kamawar jirgin da wuta.

Sashen Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ya bayyana cewa: Jirgin Ruwan dakon man fetur din ya kama da wuta ne yana ɗauke da ganga mai 750,000 na ɗanyen mai sakamakon ƙoƙarin da ya yi na ketare wata hanya da ba a ba da izini ba a jiya da rana, ya yi watsi da gargaɗin Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC, kuma ya afka cikin tarkon nakiyar da ke cikin ruwa, wanda ya haifar da fashewa da tashin gobara mai tsanani.

Iran

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted