Bayanai daga Falasdinu na cewa fiye da Falasdinawa 100 ne aka kashe bayan harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke matsugunin ‘yan gudun hijira a gabashin zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Wafa ya rawaito cewa, sama da mutane 100 ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a safiyar Asabar din nan bayan da sojojin Isra’ila suka kai hari a makarantar al-Tabi’in da ke unguwar al-Daraj a gabashin birnin Gaza.
A cewar majiyoyi jiragen yakin Isra’ilar sun yi ruwan bama-bamai a makarantar a lokacin da Jama’ar wurin ke gudanar da Sallar Asuba.
Sanarwar da ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya fitar ta ce: “Hare-haren da Isra’ila ta kai kan mutanen da suka rasa matsugunansu a lokacin da suke gudanar da sallar Asuba (Asubah), kisan kiyashin da gwamnatin mamayar ke ci gaba da gudanarwa.
Ofishin yada labaran ya yi Allah-wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi da kakkausar murya, yana mai kira ga duniya da ta yi Allah-wadai da shi, tare da dora wa gwamnatin mamaya da gwamnatin Amurka alhakin kai wannan kazamin harin bam.
Rundunar sojojin mamaya na Isra’ila ta tabbatar da harin a wata sanarwa da ta fitar kuma ta ce makarantar ta kasance maboyar kwamandojin Hamas.