Isra’ila ta kai harin bam a tsakiyar birnin Beirut da sanyin safiyar Alhamis, inda ta kashe akalla mutane shida, bayan da sojojinta masu mamaya suka ga mafi munin rana a gagarumin artabun da ba su taba ganin irinsa ba a fagen daga tsakaninsu da kungiyar Hezbollah ta Lebanon a cikin shekara guda.
Akalla mutum shida ne suka mutu sannan bakwai suka jikkata, in ji jami’an kiwon lafiya na kasar Lebanon.
Shaidu sun ba da rahoton jin karar fashewar wani katon bam kuma wata majiyar tsaro ta ce Isra’ila ta kai hari kan wani gini da ke tsakiyar birnin Beirut a unguwar Bachoura da ke kusa da majalisar dokokin kasar, a kusa da ofishin gwamnatin Lebanon.
Har ila yau, sun kai harin makami mai linzami uku a yankin kudancin Dahiyeh, inda aka kashe shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah a makon da ya gabata, an kuma ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi kamar yadda jami’an tsaron kasar Labanon suka sanar.
Hezbollah ta ce ta yi arangama da sojojin Isra’ila da suka yi kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon, tare da kai hari kan sojojin Isra’ila da ke kan iyakar kasar, a cewar sanarwar da kungiyar ta fitar.
Sojojin Isra’ila dai sun sanar da mutuwar sojojinsu takwas a wani farmakin kasa da suka kai kudancin Lebanon
Sojin Isra’ilar sun kuma bayar da rahoton jikkatar sojojinsu da dama da suka shiga Lebanon.