Wani Bafalasdine guda ya yi shahada sakamakon harin sojojin mamayar Isra’ila a birnin Al-Bireh da ke Yammacin Kogin Jordan
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta sanar a ranar Talata cewa: Wani Bafalasdine mai suna Ziyad Muhammad Jabir, mai shekaru 54, ya yi shahada sakamakon harbinsa da bindiga da sojojin mamayar Isra’ila suka yi a unguwar Umm al-Sharayet da ke al-Bireh a tsakiyar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce Jabir ya yi shahada ne sakamakon raunukan da ya samu lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai masa hari a unguwar.
Tun da farko dai, ƙungiyar masu bada agaji ta Falasɗinu ta Red Crescent ta ba da rahoton cewa: Ma’aikatanta sun yi wa wani mutum da ke da raunukan harbi a cinya magani, inda ta bayyana yanayinsa a matsayin “mai matuƙar tsanani.”
Ta ƙara da cewa ma’aikatanta sun yi aikin CPR kafin a kai shi asibiti. Da mutuwar Jabir, adadin Falasɗinawan da sojojin mamayar Isra’ila suka kashe a Yammacin Kogin Jordan ya haura 100 tun farkon wannan shekara, a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare, kan fararen hula