Wani Bafalasdine Ya Yi Shahada A Harin Da Aka Kai Zirin Gaza

Wani Bafalasdine yayi shahada sannan wasu uku sun jikkata sakamakon wani hari da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a birnin Gaza Wani Bafalasdine ya yi

Wani Bafalasdine yayi shahada sannan wasu uku sun jikkata sakamakon wani hari da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a birnin Gaza

Wani Bafalasdine ya yi shahada kuma wasu uku na daban sun jikkata sakamakon wani harin wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a unguwar Rimal da ke yammacin birnin Gaza.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Wani jirgin saman Isra’ila mara matuki ciki ya kai hari kan masu wucewa kusa da filin wasa na Falestinu da ke unguwar Rimal.

Majiyoyin lafiya a Asibitin Al-Shifa sun ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da kuma jikkatan wasu uku, daya daga cikinsu raunnsa ya tsananta.

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-haren sama kan yankin Gaza da suka lalata, wanda hakan ya karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki tun daga ranar 10 ga watan Oktoban shekara ta 2015.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted