Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka ce ke da alhakin rashin tsaro a mashigar ruwan Hormuz
Gholam Huissein Darzi, wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya yana bayyana munanan matakan wuce gona da iri da sojojin Amurka ke dauka kan jiragen ruwan Iran da kuma toshe hanyoyin shigewar jiragen ruwa da ke cikin tashoshin jiragen ruwan kasar.
Huissein Darzi ya jaddada cewa: Alhakin bullar duk wani rikici a kan hanyoyin jiragen ruwa ya rataya ne a wuyan masu kai hari, kuma takunkumin jiragen ruwa da aka sanya wa Iran ya saba wa Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kuma alama ce ta hukunci ga fararen hula.
Ya jaddada cewa alhakin duk wani rikici a kan hanyoyin jiragen ruwa ya rataya ne kai tsaye kan masu kai hari da masu goyon bayan ayyukan ta’addanci kan Iran.
Wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kuma soki takunkumin jiragen ruwa da aka sanya wa tashoshin jiragen ruwan kasar Iran, ya kuma jaddada cewa: Amurka ta sanya takunkumi kan duk wani zirga-zirgar jiragen ruwa da ke cikin tashoshin jiragen ruwan Iran da tashoshin jiragen Ruwan da suke kasashen waje tun daga ranar 12 ga watan Afrilu.
Darzi ya jaddada illolin jin kai da wannan mataki zai haifar, inda ya bayyana cewa toshe hanyoyin ruwa da Amurka ta yi yana barazana ga damar da fararen hula ke da ita ta samun abinci, magunguna, man fetur, da sauran kayayyakin buƙata na yau da kullum.