Hamas: Manufar Kai Harin Ambaliyar Al-Aqsa Kan Isra’ila

Harin Ambaliyar Al-Aqsa da Falasdinawa suka kai kan Isra’ila ya rusa karyar karfin fannin dabarun tsaro da leken asirin Yahudawan Sahayoniyya Youssif Hamdan, wakilin ƙungiyar

Harin Ambaliyar Al-Aqsa da Falasdinawa suka kai kan Isra’ila ya rusa karyar karfin fannin dabarun tsaro da leken asirin Yahudawan Sahayoniyya

Youssif Hamdan, wakilin ƙungiyar Hamas a Aljeriya, ya tabbatar da cewa: “Guguwar Ambaliyar Al-Aqsa” ta samo asali ne daga mamayar da Haramtacciyar kasar Isra’ila da take yi ga yankunan Falasdinawa da kuma cin zarafin da take y ikan al’ummar Falasdinu, a gaskiya, cewa wannan hari na Ambaliyar Al-Alqa ya zama wani babban koma-baya ga tsarin tsaron Isra’ila da kuma tsarin sojanta, kuma ya bayyana ikon ‘yan gwagwarmaya na shiga kutsa kai cikin mafi fifikon tsaron ‘yan mamayar Isra’ila.

Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya ruwaito cewa: Da wayewar ranar Asabar, 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun ƙaddamar da wani kakkaran hari na tarihi, mai suna “Ambaliyar Al-Aqsa” a Zirin Gaza, na ɗan lokaci, gami da kai hare-haren ƙasa da na teku don bincike da ceto ‘yan gwagwarmaya a matsugunan Yahudawa da dama.

Mohammad Al-Da’if, kwamandan rundunar Izzuddin Al-Qassam, reshen soja na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas), ne ya sanar da wannan aikin, kuma ya ɗauki wannan aikin a matsayin babban hari kan ƙungiyar Yahudawan Sahyoniyya da ta dauki tsawon shekaru da dama tanacin kareta babu babbaka kan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted