Cibiyar wacce take kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta fitar da bayanin dake cewa, tun bayan da Amurka ta sanar da killace tasoshin jiragen ruwan Iran, manyan tankokin ruwan na dakon mai 34 mallakin Iran ne su ka tsallake wannan ketarewar zuwa kasuwannin duniya.
Sanarwar ta ce, a kalla 6 daga cikin wadannan tankokin dakon man fetur din na ruwa suna dauke da danyan mai da kudinsa ya kai dala miliyan 10.7.
Daga cikin wadannan jiragen ruwan dakon man da akwai Babban jirgin ruwa na ” Dorina” wanda yake dauke da tutar Iran, ta kuwa yi nasarar ketare killacewar ta Amurka,bayan kashe na’urar dake aika sakwanni akan wurin da jirgi yake tafiya.
Jaridar “Financial Times; ta nuna wasu hotunan tauraron dan’am da ta ce na jirgin ruwan ne da yake sauke man dake cikinsa a kasar Malysia.
Wasu daga cikin jiragen ruwan na Iran da suke ci gaba da zirga-zirgar jiragen man kasar zuwa kasuwannin duniya sun hada da “Alisia” da “Morlikishan” da Amurka ta kakaba musu takunkumai.
Iran tana zargin Amurka da cewa killace tasoshinta na ruwa da ta yi, ba su kan dokokin kasa da kasa.
Amurka ta rike wasu jiragen ruwan Iran biyu, daya ta dakon kaya da kuma ta dakon man fetur. Iran ta ce, abinda Amurkan take yi fashi ne da makami da doron ruwa.