Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da yin mu’amala da kasashen nahiyar Afirka amma ba da salo irin na ‘yan mulkin mallaka ba.
Shugaban kasar ta Rasha ya kara da cewa, alakar kasarsa da nahiyar Afirka za a gina ta ne akan hanyoyin ci gaba ba kamar yadda ‘yan mulkin mallaka su ka yi ba, na wawashe dukiyar nahiyar.
Haka nan kuma shugaban kasar ta Rasha ya ce; Batu mai muhimmanci wanda nake son jaddadawa wanda kuma muke tattaunawa tare da takwarorina, shi ne Afirka tana albarkatu masu yawan gaske,kuma tana da mutane da yawa matasa, sannan kuma al’ummar nahiyar suna karuwa ne.”
A ranar Litinin din da ta wuce ne aka bude taron shekara-shekara na “Valdai” da shugannin kasashe fiye da 40 suke halarta a birnin Moscow wanda kuma ya ci gaba har zuwa jiya 1 ga watan Oktoba.
Taron wanda shi ne karo na 23 ya kunshi tawagogi daga kasashen nahiyoyin duniya mafi yawanci daga Asiya da kuma Afirka.