Mataimakiyar shugaban Venezuela Delcy Rodriguez ta zargi Amurka da sace Shugaba Nicolas Maduro, tana mai watsi da duk wani ikirari da ke cewa cire shi daga mukamin ya canza shugabancin Venezuela.
Rodriguez ta zargi Amurka da sace Shugaba Nicolas Maduro da nufin kwace ikon kasar da albarkatun kasa.
Da take magana a gidan talabijin na gwamnati, Mataimakiyar shugaban kasar Delcy Rodriguez ta ce ayyukan Washington sun nuna cewa ainihin manufar wannan aiki shi ne wargaza ‘yancin siyasa na Venezuela da kuma sake mayar da mulkin mallaka.
Rodriguez ta bukaci a saki Maduro da matarsa, Cilia Flores nan take.
A ranar Asabar ne dai Amurka da kama shugaba Maduro da matarsa bayan kaddamar da manyan hare-hare a kasar.
Amurka ta gurfanar da Maduro kan tuhumar zargin safarar miyagun kwayoyi da makamai.
Tuni shugaban Amurka, Donald Trump ya ce kasarsa za ta ci gaba da jagorantar Venezuela har zuwa lokacin kafa gwamnati.