Duniya na tir da Amurka kan keta dokokin kasa da kasa a Venezuela

Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da Amurka kan keta dokokin kasa da kasa a Venezuela. Firaministan Spain ya ce abun tir ne ” karya dokokin duniya a Venezuela. Finland ta yi kira da a mutunta dokokin kasa da kasa bayan matakin Amurka a Venezuela. Shugaban kasar Finland Alexander Stubb ya ce […]

Venezuela ta ce har yanzu Maduro ne ‘shugaban kasar’

Mataimakiyar shugaban Venezuela Delcy Rodriguez ta zargi Amurka da sace Shugaba Nicolas Maduro, tana mai watsi da duk wani ikirari da ke cewa cire shi daga mukamin ya canza shugabancin Venezuela. Rodriguez ta zargi Amurka da sace Shugaba Nicolas Maduro da nufin kwace ikon kasar da albarkatun kasa. Da take magana a gidan talabijin na […]

Magajin Garin New York Ya Yi Allah Wadai Da Harin Amurka Kan Venezuela

Magajin Garin New York Zohran Mamdani ya yi Allah Wadai da Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump da kai hari kan Venezuela, yana mai cewa harin sauyin gwamnati ya zama “ayyana yaki” kuma ya karya dokokin kasa da kasa. Mista Mamdani ya yi wannan furucin ne a cikin wani sako, bayan da sojojin Amurka suka kai […]

Hamas ta la’anci harin da Amurka ta kai wa Venezuela

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai wa Venezuela da kuma kame Shugaba Nicolás Maduro, tana mai bayyana shi a matsayin “kai hari kan ikon mallakar kasa mai ‘yanci.” “Wannan harin yana wakiltar ci gaba da manufofin Amurka marasa adalci da tsoma baki, wanda burinsu na mulkin […]

Zanga-Zanga Ta Barke A Amurka Kan Aikin Sojen Trump A Venezuela

Masu zanga-zanga sun kwarara kan titunan biranen Amurka suna allawadai da aikin sojen da gwamnatin shugaba Trump ta ke yi a kasar Venezuela da kuma da kuma kama shugaba Madoro da matarsa Cilia Flores. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zanga a mafi yawan biranen Amurka suna nuna damuwarsu da wani […]

Iran Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Kasar Venezuela Bayan Harin Amurka

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana tir da allawadai da hare-haren da sojojin Amurka suka kai kasar Venezuela a jiya Asabar sannan ya ce gwamnatin kasar Iran tana goyon bayan mutanen kasar Venezuela da gwamnatinsu. A wata hira tsakaninsa da tokwaransa na kasar Venezuela Yyan […]

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Yayin Magana Da Jakadan Iran A Caracas

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Baqaee ya zanta ta wayar tarho da jakadan kasar a birnin Caracas Ali Chegni wanda ya bayyana masa irin halin da ake ciki a kasar. Ya kuma bayyana masa yadda al-amura suke tafiya a kasar bayan hare-haren da Amurka ta kai kan kasar da kuma sace shugaban kasa […]

Kasashen Liberia Da DRC Sun Zama Sabbin Mambobin Kwamitin Tsaron MDD

Kwamitin tsaro na MDD ya yi maraba da sabbin mambobin da ba su da hakkin hawa kujerar naki, da su ka hada Bahrain, Columbia, DRC, Lativa da kuma Liberia. Kasashen biyar da suka shiga kwamitin za su zauna ne har na tsawon shekaru biyu kafin a sake zabar wasu. Kasar DRC ta shiga cikin kwamitin […]

 Sheikh Kassim Ya Yi Kira Da A Bai Wa Sojojin Kasar Lebanon Makamai

jagoran Hizbullah

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheik Na’ima Kassim ya yi kira da a bai wa sojojin kasar makamai, sannan kuma a gudanar da zabuka a lokacinsu. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi na tunawa da shahadar Shahid Kassim Sulaimani da kuma  Injiniya Abu Mahdi a jiya da marece a birnin Beirut […]

 Trump: Mu Za Mu Mulki Venezuela Har Zuwa Lokacin Zabe

Shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda ya gabatar da taron manema labaru a jiya ya bayyana cewa Amurka za ta Mulki kasar ta Venezula har zuwa lokacin yin zabe. Shugaba Donald Trump wanda ya gabatar da taron hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen kasar, ya bayyana cewa; abinda zai biyo bayan kama shugaban kasar […]

Ministan Tsaron Venezuel: Za Mu Yi Nasara Akan Amurka

A matakin farko na mayar da martani akan abinda ya faru, Ministan tsaron kasar ta Venezuela Vladimir Padrino López ya sanar da shiga halin ko-ta-kwana a fadin kasar. Haka nan kuma ya ce; kasar za ta yi aiki da dukkanin karfin da take da shi domin kare ‘yancinta da huruminta. Ministan tsaron na kasar Venezuela […]