Ministan harkokin waje na kasar Venezuela ya bukaci MDD ta takurawa gwamnatin kasar Amurka ta sallami shugaba Nicolas Madoro da matarsa Cilia Flores wadanda suke tsare a birnin News.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a gaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD a jiya litinin a birnin Geneva. Ya kuma kara da cewa, sojojin Amurka sun sace shugaba Madoro da matarsa a ranar 3 ga watan Jeneru na wannan shekara a birnin Caracas babban birnin kasar. Bayan sun kashe mutane fiye da 100.
Labarin ya kara da cewa a halin yanzu Madoro da matansa suna tsare a birnin New York suna kuma jiran sharia. Tuni dai a zamanta na farkon kotun ta saurari karar da gwamnatin Amurka ta shigar kan shugabankasar ta matarsa. Amma duk sun musanta laifin.
Bayan haka dai gwamnatin kasar Venezuela ta zabi bude kofar tattaunawa da kasar Amurka don warware matsaloli tsakanin kasashen biyu. Gwamnatin Amurka tana zargin Madoro da matarsa da laifin jagorantar wata kungiyar fasakorin miyagun.