Velayati: Taron Malaman Yahudu A Azerbaijan Tsokana Ce Ga Musulmi Shia

Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci  shawara Ali Vilayati  ya yi allawadi da kasar Azerbaijan kan shirya taron yahudawan turai a kasar a

Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci  shawara Ali Vilayati  ya yi allawadi da kasar Azerbaijan kan shirya taron yahudawan turai a kasar a cikin watan Nuwamba mai zuwa, kuma ya bayyana taron a matsayin tsokanace ga musulmi da kuma addinin musulunci, kuma ba zai je ko ina ba.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Vilayati yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa , wannan shi ne karon farko wanda aka taba gudanar da taron yahudawan duniya a birnin Baku na kasar Azerbaijan, kasa ta musulmi shia.

Ya ce, wannan shi ne karon farko wanda aka gudanar da taron yahudawan duniya a kasar musumi shia, kuma kowa ya san cewa, taron tsokanane ga musulmi musamman shia saboda.

Valayati ya bayyana cewa, taron yana son jawo kasashen musulmi a cikin hadakan addinin Ibrahimiyya da suke fada, kuma kokari ne na hada fada tsakanin musulmi da yahudawa.

Kasar Azerbaijan dai tana matso wa zuwa yahudawa da wadanda ba musulmi ba, don ingiza mutanen kasar musulmi su nuna rashin amincewarsu sai ta dira a kansu da sunan wadanda basa son yahudawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted