UNRWA ta bukaci Isra’ila da ta bari a shigar da kayan agaji a Gaza

UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a

UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin.

“Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin da lokaci yake kara kurewa, tasirin haramcin yana karuwa a Gaza.

Lazzarini ya kara da cewa “akwai hadarin komawa ga yanayin da muka fuskanta watannin da suka gabata, game da kara yaduwar yunwa a tsakanin mutanen  zirin Gaza sakamakon matakan da Isra’ila take dauka.

“Isra’ila” ta sanar da dakatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza a ranar 2 ga Maris, tare da yin barazanar kara matsin lamba kan Hamas, yayin da bangaren ‘yan gwagwarmayar  Falasdinu ya ki amincewa da shawarar Amurka na tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta farko, maimakon shiga mataki na biyu kamar yadda yarjejeniyar tanada tun daga farko.

A wani mataki na baya-bayan nan na kara matsa lamba kan al’ummar zirin Gaza, Ministan Makamashi na Isra’ila Eli Cohen ya sanar da cewa, ya rattaba hannu kan wata doka ta katse wutar lantarki a yankin Gaza daga ranar 9 ga Maris, yana mai jaddada cewa “Isra’ila za ta yi amfani da dukkan kayan aikinta wajen  dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma tabbatar da kawo karshen samuwar Hamas a cikin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments