Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta ce hare-haren da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin da ke gabar yammacin Kogin Jordan da ta mamaye ya janyo asarar rayukan akalla iyalai 2,000 daga tsakiyar watan Disamba.
Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da wani mummunan tashin hankali a kan Falasdinawa a birnin Jenin da ta mamaye a ranar Talata, kwanaki biyu kacal bayan da aka tsagaita bude wuta a Gaza domin kawo kwanciyar hankali a yankin Falasdinawa.
Shugaban hukumar Friedrich ya ce a halin yanzu, hukumar ba za ta iya ba da “cikakkun ayyuka ga sansanin” saboda karuwar tashe-tashen hankula da sojojin gwamnatin kasar da ‘yan kaka-gida ba bisa ka’ida ba ke yi kan Falasdinawa.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, akalla mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu 35 suka jikkata a harin da aka kai ranar Talata.
M. Friedrich ya ce harin na baya-bayan nan da aka kai a sansanin “yana yin barazanar ruguza yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanaki kadan da suka gabata a Gaza.”
Falasdinawa da yawa dole ne su fice daga sansanin a yanzu yayin da sojojin Isra’ila suka ba da tilastawa yin kaura.
Yakin kisan kare dangi na Isra’ila a zirin Gaza ya kashe mutane fiye da 47,000 da suka hada da mata da kananan yara.