Unifel: Tel Aviv Tana Keta Kuduri Mai Lamba 1701 A Lebanon

Dakarun MDD na tabbatar da zaman lafiya a kudancin Lebanon sun zargi Isra’ila da cewa tana keta kudurin MDD mai lamba 1701 akan yarjejeniyar tsagaita

Dakarun MDD na tabbatar da zaman lafiya a kudancin Lebanon sun zargi Isra’ila da cewa tana keta kudurin MDD mai lamba 1701 akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.

Rndunar ta UNIFEL ta fitar da wani bayani da a ciki ta ce Isra’ilan tana kai hare-hare domin rusa da lalata dukiya da gine-gine a kudancin Lebanon da hakan keta kuduri mai lamba ta 1701 ne na tsagaita wutar yaki da kuma dokokin kasa da kasa.

Bayanin ya cigaba da cewa: Da safiyar Asabar rudnunar ta UNIFEL ta ga motar buldoza ta sojojin Isra’ila tana tunkude wani shinge na duro da aka sanya akan layin  dake tsakanin Lebanon da Isra’ila a yankin Labbunah. Haka nan kuma sun tunkude hasumiyar hangen nesa ta sojojin Lebanon dake kusa da sansanin UNIFEL.’

Rundunar ta kuma ce wannan abinda Isra’ilan ta yi, yana cin karo da kudurin MDD mai lamba 1701, da kuma dokokin kasa da kasa.

A wani labarin mai alaka da wannan Isra’ilan tana bayyana cewa, ba ta da shirin ficewa daga Lebanon bayan kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki kamar yadda yaryeyeniyar ta bukata.

Sai dai kuma a gafe daya kungiyar Hizbullah ta bakin babban sakatarenta ta ce, ita ce za ta ayyakan lokacin mayar da martani akan keta yarjejeniyar da HKI take yi,tare da zabar lokacin da ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments