UNICEF: Yaran Gaza suna rayuwa karkashin ta’addancin Isra’ila

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa yara a yankin Zirin Gaza da aka yiwa kawanya suna rayuwa cikin firgici,

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa yara a yankin Zirin Gaza da aka yiwa kawanya suna rayuwa cikin firgici, sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a kan al’ummar yankin.

Kakakin UNICEF James Elder ya ce lamarin yara da iyalai a Gaza na kara tsananta a kullum.

“Al’amarin yara a Gaza yana kara tabarbarewa a kowace rana, tare da tsananin zafi da iyalai da ke cunkushe cikin tanti a kan yashi,” in ji shi.

Ya jaddada cewa, “tare da hana shigar da kayan agaji, sama da kwanaki 250 a yakin Gaza, mutanen Gaza na fuskantar matsananciyar wahala wajen samun abinci ga ‘ya’yansu.”

Ya kuma bayyana cewa kusan yara 3,000 da ke fama da tamowa na fuskantar barazanar mutuwa a idon iyalansu a Gaza.

Ya ce, “Akwai yara 3,000 da muke ba agajin gaggawa na abinci, kuma yanzu ba mu san inda suke ba.

A gefe guda kuma, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu UNRWA ta ce sama da yara 50,000 a zirin Gaza na bukatar a yi musu jinya cikin gaggawa saboda rashin abinci mai gina jiki.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a baya-bayan nan ta ce “tare da ci gaba da takaita ayyukan jin kai, mutanen Gaza na ci gaba da fuskantar matsananciyar yunwa.”

“Hukumar UNRWA tana  aiki tukuru don kaiwa iyalai agaji amma lamarin yana fuskantar tarnaki,” in ji hukumar.

Hare-haren da sojojin Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza na yin mummunar barna ga kananan yara.

Fiye da yara 14,000 ne aka bayar da rahoton cewa an kashe a tsawon watanni da Isra’ila ta kwashe tana kai hare-haren wuce gona da iri kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar a cikin wani bayani.

Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 37,300.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments