Unicef :  Yara sama da 100 aka kashe tun bayan tsagaita wuta a Gaza

Asusun kula da yara na MDD, wato Unicef, ya bayyana cewa yara sama da 100 ne suka rasa rayukansu tun bayan cimma yarjeejniyar tsagaita wuta

Asusun kula da yara na MDD, wato Unicef, ya bayyana cewa yara sama da 100 ne suka rasa rayukansu tun bayan cimma yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza.

Tun lokacin da aka fara tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoba, 2025, an kashe yara sama da 100 a Gaza, kwatankwacin kusan yaro daya a kowace rana inji Unicef.

Har yanzu lamarin rayuwa bai daidaitu ba a Gaza inji kungiyoyin agaji, duk da cewa hare –haren bama-bamai da harsasai sun dan ragu a lokacin tsagaita wutar, amma ba su tsaya ba.

Yawaicin mace macen na faruwa ne ta hanyar hare-haren jiragen sama da jiragai masara matuka, ” in ji James Elder, mai magana da yawun UNICEF, a lokacin taron manema labarai na yau da kullun na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.

Mista Elder ya jaddada cewa karin yara sun mutu sakamakon yanayin hunturu mai tsanani.

A saboda haka UNICEF, ta bukaci a bude hanyoyin samun taimako, kara yawan kwashe yara daga yankin, da kuma tabbatar da cewa wannan shi ne “lokacin da kisan yara a Gaza zai kare.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted