Fezeshkiyan Ya Shaidawa Takwaransa Na Rasha, Isra’ila Na Da Hannu Kai Tsaye A Rikicin A Iran

shugaban kasar iran Masoud Pezeshkiyan da na rasha Viladmir Putin sun tattauna ta wayar tarho a yau juma’a inda suka yi tsokaci game da tarzomar da ta faru a kasar Iran a baya bayan nan, da kuma batun ci gaban yanki da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. wannan shi ne karon farko da aka tattaunawa […]
Falasdinawa 12 Suka Mutu A Wani Sabon Hari Da HKI Ta Kai A Yankin Gaza

rahotanni sun bayyana cewa akalla falasdinawa 12 ne suka mutu yayin da wasu guda 18 kuma suka jikkata a wani sabon hari da HKI takai a fadin yankin Gaza a cikin Saoi 24 , a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra’ila ke yi da aka cimma tsakaninta da kungiyar gwagwarmaya […]
Gwamnatin Tarayya Na Kokari Wajen Gina Rundunonin Tsaro Masu Karfi Da Inganci

Ministan Tsaron Nigeriya , Janar Christopher Musa mai ritaya, ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na gina ingantattun rundunonin soji, dake cike da Kwararru da kuma juriya, domin kare martabar Nijeriya da kuma tallafa wa wajen ci gaban kasa. Musa ya bayyana haka ne a wajen bude taron karawa juna sani na kasa, wanda aka shirya; […]
Alummar Iran Sun Dakile Makircin Makiya Da Zanga-zangar miliyoyin alummar Kasar

shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen ya fadi cewa kasar Amurka da isra’ila sun aike da wakilansu domin tayar da tarzoma a iran inda suka kona masallatai suka kuma kashe jami’an tsaro , sai dai Alummar iran sun mayar musu da martani ta hanyar shirya gagarumar zanga-zangar ta miliyoyin mutane a fadin kasar. Sayyid Abdulmalik […]
Kasashen Iran Da Rasha Da China Sun Tir Da Tsoma Bakin Amurka Kan tarzomar Da Aka Yi A Iran

rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta caccaki Amurka a lokacin zaman gaggawa na kwamatin tsaro na majalisar dinkin duniya, kuma ta zargi Amurka da hannu wajen tayar da tarzoma da karkatar da zanga-zangar lumana da aka yi, suma kasashen rasha da china sun yi watsi da tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin cikin gidan […]
Amurka Ta Dorawa Shugaban Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran Takunkuman Tattalin Arziki

Ma’aikatan baitul mali Amurka ta dorawa Dr Ali Larijani babban sakataren hrkokin tsaron kasar Iran takunkuman tattalin da kuma wasu kwamandojin sojojin kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa, sun dorawa wadan nan jami’an tsaron […]
Mutane A Birnin Tehran Sun Koma Kan Rayuwarsu Da Suka Saba

Bayan tashe-tashen hankula wadanda suka mamaye kasar Iran saboda yan ta’adda wadanda Amurka da HKI suke taimakawa a cikin kasar a halin yanzu mafi yawan harkokin rayuwa sun koma kamar yadda suke a birnin Tehran da sauran birani a kasar. A ranar 12 ga watan Jenenrun da muke ciki aka fara zanga-zangar lumana a babbar […]
Unicef : Yara sama da 100 aka kashe tun bayan tsagaita wuta a Gaza

Asusun kula da yara na MDD, wato Unicef, ya bayyana cewa yara sama da 100 ne suka rasa rayukansu tun bayan cimma yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Tun lokacin da aka fara tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoba, 2025, an kashe yara sama da 100 a Gaza, kwatankwacin kusan yaro daya a kowace rana […]
Iran, Rasha, da China sun yi Allah wadai da Amurka kan haddasa tarzoma a Iran

Kasashen Iran Rasha da kuma China, sun yi tir da Amurka kan ingiza masu zanga zangar data rikide zuwa tarzoma a Iran. Mataimakin Wakilin Iran na Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamhossein Darzi, ya soki Amurka sosai a yayin taron gaggawa na Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan tarzomar da kasashen waje suka haddasa a […]
Iran ta musanta rahotanni shirin zartar da hukuncin Kisa kan wani dan zanga zanga

hukumomin shari’a na Iran sun musanta rahotannin dake cewa ana shirin aiwatar da hukuncin kisa kan wani matashi da aka kama cikin bata-gari da aka kama yayin zanga zangar lumana da makiya suka rura ta rikide zuwa tarzoma a kasar. An kama Erfan Soltani, mai shekaru 26, a ranar 10 ga Janairu a lokacin tarzomar, […]
Pezeshkian : Gwamnati na ta kudiri anniyar yaki da matsin attalin arziki da rashawa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar warware matsalolin da suke tasowa na matsin tattalin arziki, cin hanci da rashawa, da rashin gudanar da harkokin kudi yadda ya kamata musamman a fannin kakkasa yadda ake kashe kudaden kasashen waje a kasar. Pezeshkian ya jaddada amincewar gwamnati ga aiwatar da shirin cikin […]