Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadi game da tabarbarewar matsalar jin kai a zirin Gaza da Isra’ila ke ci gaba da yi wa kawanya.
Kakakin hukumar James Elder ya yi gargadin cewa, yara da dama da ke kwance a asibiti masu fama da matsananciyar yunwa ba za su iya rayuwa a mako mai zuwa ba idan har Isra’ila ta ci gaba da kafar ungulu da ayyukan jin kai a yankin.
A wata hira da yayi da gidan talabijin na Sky News, James Elder ya bayyana mummunan halin da ake ciki a Gaza da kuma sadaukarwar da iyaye mata suke yi don ciyar da ‘ya’yansu.
Wannan lokaci shi ne mafi wahala da mata da yara suka taba fuskanta a Gaza inji shi.
Ya ba da shaida ga yadda ya gamu da yaran da ke kwance a asibiti, wadanda rayuwarsu ke fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki.
Rahotanni daga kungiyoyin da ke da alaka da Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin jin kai sun bayyana lamarin da mai ban tsoro.
Kungiyoyin ba da agaji sun yi gargadin cewa, idan ba a dage shingen da Isra’ila ta yi ba nan ba da jimawa ba, al’ummar kasar na cikin hadarin fadawa cikin wani bala’in jin kai da ba a taba gani ba.