UNICEF Tayi Gargadi Game Da Makomar Matasan Labanon

hukumar UNICEF ta yi gargadi game da makomar matasan labanon saboda hare haren da isra'ila da amurka ke kai wa

Hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF  ta yi  rahoton cewa hare -haren da isra’ila ke kai wa a kasar labanon tun daga watan maris kimanin yara 261 suka mutu kuma yayi sanadiyar jikkatar wasu 1056.

Hukumar UNICEF ta tattara bayanai game da mummunar barna da aka tafka kan ilimi tare da asarar rayuka da kuma raunukan da aka samu, kimanin cibiyoyin ilimi 436 ne suka lalace ko kuma aka ruguza su baki daya,  lamarin da ya kara sanya kusan yara 100,000  cikin hadarin rashin samun ilimi, bugu da kari an kashe malamai 86 ko kuma suka samu raunuka

Kamar yadda hukumar ta Unicef ta bayyana akalla kashi 80 cikin dari na iyalai sun fuskanci matsaloli masu yawa wajen samun muhimman abubuwan da suke bukata, don haka kungiyar ta yi gargadin cewa tabarbarewar yanayin zamantakewa da tattalin arziki na kara jefa yara zuwa ga rashin tabbas na samar da abin da za su ci, da kuma barin makaranta

hare haren da isra’ila ta kai a kasar labanon yayi sanadiyar mutuwar mutane 4386 tare da jikkata wasu guda 12407 da kuma tilsatawa sama da miliyan daya barin gidajensu ba shiri tun daga ranar 2 ga watan maris kamar yadda gwamnatin labanon ta bayyana

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted