Ukraine ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 30

Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har

Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a jiya Talata ce ta tabbatar da hakan, bayan sassan biyu sun shafe sa’o’i suna tattaunawa.

Sanarwar ta ce akwai yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, kuma Amurka za ta tuntubi Rasha kasancewar amincewarta zai tabbatar da cimma nasarar matakin.

Baya ga hakan, Amurka ta amince da dage matakin dakatar da musayar bayanan sirri, kuma za ta ci gaba da baiwa Ukraine tallafin tsaro, yayin da kuma sassan biyu suka tattauna kan muhimmancin aiwatar da matakan samar da tallafin jin kai, musamman a wa’adin tsagaita bude wutar.

Har ila yau, masu shiga tsakanin sun amince da samar da tawagogin da za su fara tattaunawa, da nufin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

 A daya hannun kuma, Amurka ta jaddada aniyarta ta hawa teburin shawara da Rasha, yayin da Ukraine ta jaddada muhimmancin shigar sauran abokan hulda na Turai cikin tsarin na cimma daidaito.

Bugu da kari, jagororin Ukraine da na Amurka, sun amince da gaggauta kaiwa karshen cikakkiyar yarjejeniyar bunkasa cin gajiya daga muhimman ma’adanan Ukraine, ta yadda za a kai ga fadada tattalin arzikin kasar. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments