Kasar Uganda ta sanar da aikewa da sojojinta zuwa birnin birnin kasar Sudan Ta Kudu, Juba saboda ba shi kariya. Sai dai har yanzu gwamnatin Sudan din ba ta tabbatar da hakan ba.
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Uganda Janar Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa; Rundunar musamman ta Ugandan ta shiga cikin birnin Juba, domin ba shi kariya.
Janar Muhoozi Kainerugaba ya kuma ce: “ Za mu kare dukkanin kasar Sudan Ta Kudu, kamar yadda za mu kare kasarmu. A wurinmu Salva Kiir ne mu ka aminta da cewa halartaccen shugaban kasar Sudan Ta Kudu,don haka duk wanda zai shelanta yaki akansa, ya shelanta yaki ne akan Uganda.”
Har ila yau janar din na Uganda ya kuma ce; “ Wadanda su ka aikata laifuka za su dandana kudarsu.”
A cikin kwanakin bayan nan an shiga dambaruwar siyasa a kasar Sudan Ta Kudu bayan da gwamnatin shugaban Salva Kiir ta kama jami’an soja da kuma na siyasa masu alaka da mataimakin shugaban kasar Reik Machar. Hakan ya biyo bayan barkewar wani sabon bore ne na ‘yan kabilar Nuer da su ka yi fada da sojojin gwamnati.