‘Yan Sandan kasar Uganda sun yi arangama da masu Zanga-zanga da suke nuna kin amicewa da sakamakon farko na zabe da hukumar zaben kasar ta sanar,wanda ya nuna cewa shugaba mai ci Yoweri Musaveni ne akan gaba.
Har ila yau ‘yan sandan sun yi kokrain kashe wutar da masu Zanga-zangar su ka kunna a kan hanyoyi, tare kuma da jefa hayaki mai sa hawaye.
A ranar zaben, an katse aikin hanyoyin sadarwa ta internet, an kuma yi jinkirin bude wuraren kada kuri’a.
Ya zuwa yanzu an nuna cewa shugaba Mosaveni yana kan gaba da kaso 70% na jumillar kuri’un daka kidaya, yayin da mai bi masa a baya Bobi Wine, ya sami kaso 19%.
Shi dai Moseveni ya dauki shekaru 40 akan karagar mulkin kasar ta Uganda.
A tsawon tarihin wannan kasa tun bayan samun ‘yanci daga mulkin mallaka a 1962, wani shugaba farar hula bai taba mika Mulki ba, sai dai a sauke shi ta hanyar juyin Mulki.