Hukumar Zabe a Uganda ta sanar da Yoweri Museveni a matsayin wanda ya sake lashe zaben shugaban kasar da kashi 71.65% na kuri’un da aka kada yayin da babban abokin hamayyarsa Bobi Wine ya samu kashi 24.72% bayan zaben na ranar 15 ga Janairu.
Roger Museveni, shugaban ƙasar Uganda tun daga shekarar 1986, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da kashi 71.65% na ƙuri’un da aka kaɗa, a cewar hukumar zaɓe. Abokin hamayyarsa, Bobi Wine, wanda sunansa na gaskiya shine Robert Kyagulanyi, ya sami kashi 24.72% na ƙuri’un.
Wannan sakamakon ya tabbatar wa Museveni dake mulkin kasar tun 1986 wani wa’adi na bakwai a jere, wanda ya tsawaita mulkinsa na tsawon kusan shekaru 40 bayan kwaskware kundin tsarin mulki da aka cire shekaru a wa’adin shugabancin kasa.
A nahiyar Afirka, Teodoro Obiang Nguema a Equatorial Guinea da Paul Biya a Kamaru ne kawai suka fi Museveni dadewa kan madafun iko.
Bayanai sun ce ba’a san inda madugun ‘yan adawa na kasar yake ba, amma a cikin wani sako a shafukan sada zumunta a wannan Asabar, ya yi ikirarin cewa ya samu tserewa daga hannun jami’an tsaro da suka kai samame gidansa.
Tun da farko, kakakin ‘yan sanda ya musanta wa manema labarai duk wani yunƙuri na kama madugun ‘yan adawan.
Ya kuma musanta zargin cewa an killace gidan Bobi Wine.
‘Yan jarida daga Agence France-Presse (AFP) sun ba da rahoton cewa an hana su shiga gidan shugaban ‘yan adawa da sanyin safiyar Asabar.