Rahotanni sun bayyana cewa wani gungun furononi iraniyawa da suka kwashe shekaru a gidan kurkukun hadaddiyar daular labarawa sun shaki iskar yanci inda aka sakesu bayan tattaunawar deplomasiya da tsaro da ta gudana tsakanin kasashen guda biyu
Kamfanin dillancin labarai na fars news ya bada rahoton cewa an saki wasu iraniyawa da ake tsare da su a gidan yarin hadaddiyar daular larabawa bayan yarjejeniyar da akayi tsakanin jami’an diplomasiya da na tsaro na iran da hadaddiyar daular larabawa,
Cikin wadanda aka saki a kwai mata kamar yadda rahoton ya bayyana sai dai bai yi karin haske kan adadin fursunonin da aka saki ba, da kuma irin laifukan da suka yi, wakilan da suka bibiyar lamarin sun sha alwashin ci gaba da kokari wajen ganin an saki sauran fursunonin iraniyawa da ake tsare da su a gidan yarin hadaddiyar daular larabawa.