Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan ya jinjina wa shugaban kasar Turkiya a kan matsayarsa dangane day akin da aka kallafawa kasar Iran.
A cikin wani bayani da y saka a shafinsa na X, Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana matsayar shugaba Rajab Tayyib Erdogan na Turkiya da kuma yadda ya yi Allah wadai da mummunar rawar da gwamnatin sahyuniya take takawa a yakin da cewa hakan abin jinjina wa ne.
Ya ce Iran da Turkiya kasashe ne makwabtan juna masu tsohon tarihi na dubban shekaru, kuma lakarsu alaka ce ta tarihi da addini da al’adu, kuma za ta ci gaba da kasancewa a haka.