Turkiya: Amincewa Da Kasar Falasdinu A Matsyin Yentacciyar Kasa Zai Kara Maida HKI Saniyar Ware
Ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya bayyana cewa karuwar yawan kasashen da suke amincewa da samuwar kasar Falasdinu mai cikeken yanci, musamman daga kasashen Turai zai kara maida HKI saniyar ware a duniya
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakaan Faidon yana fadar haka a birnin Caracas babban birnin kasar Venezuela a lokacinda yake ganawa da tokwaransa na kasar Iwoon Giil a jiya Alhamis.
Hakaan Faidon ya kara da cewa, lokaci yayi da kasashen duniya zasu amince da kasar Falasdinu a matsayin yentacciyar kasa, kuma idan amincewa da ita ya ci gaba da yaduwa a duniya wannan zai kara maida HKI saniyar ware sannan zai zama mata dole ta amince da abinda mafi yawan kasashen duniya suka amince da shi.
A ranar Laraba 22 ga watan Mayu da muke ciki ne kasashen Norway, Espania da Ireland suka bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu a matsayin cikekkiyar kasa mai zaman kanta, wanda ya jawo cece-kuce a tsakanin kasashen turai da dama.